Isra’ila za ta mamaye ilahirin Zirin Gaza ya koma karkashinta – Netanyahu

Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya ce kasarsa ta kammala shirin amfani da sojoji wajen mamaye ilahirin Zirin Gaza na Falasdinawa domin ya koma karkashin ikonta.

Isra’ila za ta mamaye ilahirin Zirin Gaza ya koma karkashinta – Netanyahu

Benjamin Netanyahu

Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya ce kasarsa ta kammala shirin amfani da sojoji wajen mamaye ilahirin Zirin Gaza na Falasdinawa domin ya koma karkashin ikonta.

A cikin wata sanarwa da ofishinsa ya fitar da safiyar Juma’a, Netanyahu ya tabbatar da shirin inda ya ce, “Sojojin Isra’ila za su shirya karbe iko da Zirin Gaza baki daya sannan a samar wa fararen hula agaji a wajen yankunan da ake gwabza yaki.”

Kazalika, wasu majiyoyi biyu daga gwamnatin Isra’ila sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa duk hukuncin da majalisar tsaron kasar ta yanke zai bukaci amincewar majalisar zartarwar kasar, wacce ita kuma ba za ta zauna ba sai ranar Lahadi.

Mamayar Gaza dai wani muhimmin mataki ne a yakin da kasar take yi a yankin na Falasdinawa wanda zai iya tilasta wa dubban mutane barin gidajensu.

Bugu da kari, dubban Falasdinawa na fama da matsananciyar yunwa saboda yadda Isra’ila ta toshe dukkan kofofin shigar da kayan tallafi zuwa yankin.

Sannan a ranar Alhamis, Netanyahu ya sanar da cewa ko da kasarsa ta kammala mamaye yankin, ba ita za ta shugabance shi ba, wasu za ta ba su rika gudanar da shi bisa kulawarta.