Jakadan Kasar Bulgaria Ya Yi Bikin Sallah A Katsina
Ambasada Yordanov ya bayyana sha’awar da kasashen duniya ke yi ga bikin sallar Jihar Katsina.
Jakadan kasar Bulgeriya a Najeriya, Yanko Yordanov, ya bi sahun daruruwan jama’a a shagulgulan bikin Sallah da aka gudanar a tsohon gidan gwamnatin Jihar Katsina.
An dai yi Hawan Bariki wanda a bisa al’adar Katsina ake gudanar da shi a rana ta biyu da Sallah, inda sarkin ya ke ziyartar gwamna a gidan gwamnati.
Wannan wata al’ada ce da aka faro tun zamanin mulkin mallaka lokacin da Turawa ke mulkin Najeriya.
Yayin hawan, Mista Yordanov ya bayyana farin cikinsa da ganin irin ƙayatattun al’adun gargajiyar Jihar Katsina.
Ya ce al’adun suna da jan hankalin masu yawon buɗe ido ƙwarai da gaske.
- Titin Legas-Kalaba: Duk kilomita 1 za ta laƙume 4bn — Minista
- Shin Ya Dace Mace Ta Fara Sitta-Shawwal Kafin Biyan Bashin Ramadan?
Ya yi tsokaci kan kamanceceniyar al’adun Jihar Katsina da na ƙasar Bulgeriya, inda ya yaba da kyakkyawan tsarin da aka gudanar.
Kasancewar Ambasada Yordanov da sauran baki daga ƙasashen waje ya bayyana sha’awar da kasashen duniya ke yi ga al’adun bikin sallar Jihar Katsina.
Bikin ya ƙunshi hakimai da daruruwan masu riƙe da sarautar gargajiya.
An yi baje kolin ado da ƙawa ta ƙasaita irin na sarauta yadda ya kamata a manyan titunan Katsina da Daura.
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Radda, ya bai wa Ambasada Yordanov da sauran masu yawon buɗe ido tabbacin tsaron lafiyarsu yayin irin wannan ziyara.
Malam Dokko ya yi alkawarin tallafa wa irin waɗannan bukukuwa a masarautun Katsina da Daura.
Ya jaddada ƙudirin gwamnatin jihar na saka hannun jari a fannin yawon buɗe ido, ilimi, kiwon lafiya, da karfafa matasa.
Ya kuma bayyana mahimmancin waɗannan bangarorin ga ci gaban jihar.