Jama’a sun yi zanga-zanga kan watsi da gyaran titi a Kano
Mazauna yankin sun ce suna da haƙƙi a gyara musu hanyar ba alfarma za a musu ba.
Mazauna Unguwar Kwari, Samegu da Gwazaye a Jihar Kano, sun gudanar da zanga-zanga kan halin da wata muhimmiyar hanya ke ciki a yankinsu.
Hanyar mai tsawon sama da kilomita 40 ta lalace, inda take cike da ramuka, kuma ta daɗe tana cikin mawuyacin hali.
- Harin sojin sama ya hallaka mutum sama da 50 a iyakar Borno da Yobe
- An kama sama da mutum 500 a zanga-zangar goyon bayan Falasɗinu a Landan
Duk da cewa an bai wa ’yan kwangila aikin sau da dama tun bayan hawan Gwamna Abba Kabir Yusuf, babu wani ci gaba mai ma’ana da aka samu.
Da yake magana a yayin zanga-zangar, shugaban al’umma Sabiu Ado, ya ce lalacewar hanyar ta jefa mazauna yankin cikin tsaka mai wuya.
Ya ce hakan ya shafi zirga-zirga, jigilar kayayyaki da harkokin kasuwanci.
Ya kuma ƙara da cewa hatsari, asarar rayuka da dukiyoyi sun zama ruwan dare.
Ya roƙi gwamnatin jihar da ta gaggauta gyaran hanyar, yana mai cewa tana haɗa ƙananan hukumomi da dama da kuma al’ummomin manoma da birni.
Ya ƙara da cewa mutanen karkara ma suna da haƙƙin samun irin waɗannan ayyukan ci gaba kamar na birane.
Mazauna yankin sun ce lalacewar hanyar ta shafi harkokin lafiya, domin marasa lafiya na wahalar isa asibiti a kan lokaci.
Mata masu juna biyu na fuskantar matsaloli sosai wajen neman kulawar lafiya.
Sun kuma koka cewa matsalar na ƙara tsananta a lokacin damina, inda wasu sassan hanyar ba za iya bin su ba, lamarin da ke kawo tsaiko wajen ƙarin kuɗin sufuri.
A yayin zanga-zangar, mazauna yankin sun ɗauki alluna ɗauke da rubuce-rubuce kamar “A gyara mana hanya, muna shan wahala,” “Lafiyarmu na cikin hatsari,” da “Gyaran hanya haƙƙimu ne, ba wata alfarma ba.”
Sun yi kira ga gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki da su ɗauki matakin gaggawa, a cewarsu gyara hanyar zai sauƙaƙa rayuwarsu tare da bunƙasa tattalin arziƙi a yankin.