Jami’an tsaro sun kori ‘yan ta’adda daga Firamaren Dangani a Katsina

Tsawon shekaru da dama babu wanda ya isa ya je ko kusa da makarantar saboda ‘yan ta’adda.

Jami’an tsaro sun kori ‘yan ta’adda daga Firamaren Dangani a Katsina

Rundunar tsaron haɗin gwiwa da ta haɗa da ta Ƙaramar Hukumar Musawa da Matazu sun samu nasarar korar ‘yan bindigar da suka mamaye firamaren Dangani na tsawon shekaru da dama.

Hakan dai na zuwa ne sa’o’i kaɗan bayan Aminiya ta rawaito yadda ‘yan bindigar suka mamaye makarantar, inda suka tilasta ɗalibai daina zuwa makarantar, lamarin da ya ƙara ta’azzara taɓarɓarewar ilimi a ƙauyukan jihar.

Mazauna garin sun bayyana wa wakilinmu cewa jami’an tsaro ne suka yi dirar mikiya a mafakar ‘yan bindigar, inda suka yi ɗauki ba daɗi da sum kuma hakan, a cewar mazauna yankin ya tilasta ‘yan ta’addan tserewa daji.

Guda daga cikin mazauna yankin, Ibrahim Lawan ya ce wannan musayar wutar ta bai wa mutanen garin ƙwarin gwiwa, bayan shafe shekaru cikin fargaba.

“Tsawon shekaru da dama babu wanda ya isa ya je ko kusa da makarantar saboda ‘yan ta’adda. Iyaye na fargabar tura yara makaranta, sannan mutane da yawa dole suka haƙura da noma.

Ita ma wata mata mai suna Aisha Gwaggo ta ce ba ƙaramin kwanciyar hankali iyaye da yara suka samu ba.

“Muna farin cikin ganin jami’an tsaro sun ɗauki mataki duk da ‘yan bindigar sun tsere. Ƙwace makamansu ya tabbatar mana gwamnati da gaske ta ke za ta kare rayukanmu.”

Ɗaya daga cikin jagororin garin da ya nemi a sakaya sunansa, ya roƙi gwamnati ta gyara musu firamaren, saboda lalacewar da ta yi.

“Harkar ilimi ta lalace saboda matsalar rashin tsaro. Amma tunda yanzu an kore su, sai gwamnati ta tallafa mana domin yaranmu su koma makaranta,” in ji shi.