Jami’in Sibiliyan JTF ya harbi kansa da bindiga a Yobe
Wani jami’in rundunar tsaro ta haɗin gwiwa ta farar hula (CJTF) ya harbi kansa da bindiga bisa kuskure a Jihar Yobe.
Wani jami’in rundunar tsaro ta haɗin gwiwa ta farar hula (CJTF) ya harbi kansa da bindiga bisa kuskure a Jihar Yobe.
Majiyoyin tsaro sun ce jami’in ya samu raunin harbin ne bayan bindigarsa ta kufce masa da misalin ƙarfe 1:00 na dare a ranar Asabar 25 ga Afrilu, 2026, a lokacin da ake kan aiki a Kuraketa da ke Ƙaramar Hukumar Damaturu.
A cewar majiyoyin, jami’in ya saki makaminsa bisa kuskure, wanda ya yi sanadiyyar rauni a ƙafarsa ta dama.
An kwashe shi nan take don neman kulawar likita kuma a halin yanzu yana cikin ƙoshin lafiya.
- Dubun ɗan banga mai yi wa Boko Haram safarar makamai ta cika a Borno
- Gobara ta lalata buhun albasa sama da 5,800 a Sakkwato
Hukumomin sun fara bincike don gano yanayin da ya haifar da lamarin.