Kannywood: Gwamnatin Kano ta rufe gidajen kallo da masu ‘downloading’

Dakatarwar ta shafi gidajen kallo, wuraren daukar hoto, masu ‘downloading’ da fim da waka da dai sauransu

Kannywood: Gwamnatin Kano ta rufe gidajen kallo da masu ‘downloading’

Hukumar Tace Finafinai da Dab’i ta Jihar Kano ta sake dakatar da dukkanin ayyukan masana’antar shirya finafinai ta Kannywood da dangoginta na tsawon makonni biyu.

Shugaban Hukumar, Abba Almustapha ya bayyana cewa wuraren da dakatarwar ta shafa sun hada da gidajen daukar hoto da gidajen kallo da wuraren downloading da sauransu.

“Gaba daya ayyukan da ake gudanarwa a wannan masana’antar za su tsaya cak na tsawon makonni biyu don masu sana’ar su zo su sabunta rajistarsu na kasancewarsu ’ya’yan wannan masana’anta,” in ji shi.

Abba Al-Mustapha ya ce daukar matakin ya zama dole, saboda shi ne kadai hanyar da zai bayar da dama da lokaci ga ’ya’yan masana’antar su sake sabunta rajistarsu kamar yadda gwamnati ta umarce su.

Ya shaida wa ’yan jarida a Kano cewa wajibi ne kowane mai gudanar da sana’a a Kannywood ya sabunta rajistarsa a cikin wadannan kwanaki don tsira da mutuncinsu.

Shugaban kungiyar jarumai da masu shirya Finafinai ta MOPPAN, Sanusi Garba Kalanbaina ya bayyana gamsuwarsu da hakan, domin a cewarsa, zai taimaka wajen ganin kowane mambansu ya sabunta rajistarsa.

“A gaskiya muna goyon bayan wannan tsari domin tun daga lokacin da aka sanar da batun soke lasisin da neman sabuntawa abin ya gagara, duba da cewa mafi yawanmu muna wajen daukar finafinai a koyaushe.

“Ina ganin wannan makonni biyun zai ishi dukkanin mutanenmu su sabunta rajistarsu.”

Ya kuma yi kira ga ’ya’yan masana’antar da su bayar da hadin kai don ganin komai ya tafi daidai.

Idan za a iya tunawa, fara aikin sabon shugaban hukumar ke da wuya ya sanar da soke lasisin duukacin masu gudanar da sana’a a Kannywood da nufin sabunta rajistar tasu.

Bin diddigi: Gaskiyar batun kai hari a Bankin CBN

NAJERIYA A YAU: Lakurawa muka kai wa hari a Sakkwato —Sojoji

Manyan alhinin Najeriya a 2024

’Yan sanda sun kama waɗanda suka shirya rikicin ‘yan daba a Kano