Kasuwar Jilli cibiyar ’yan ta’adda ce — Buratai
Buratai ya ce, duk da an sha rufe kasuwar, amma ’yan ta’adda suna ci gaba da amfani da ita tare da goyon bayan wasu da ke cinikayya da su.
Tsohon Babban Hafsan Sojojin Ƙasa na Najeriya, Laftanal Janar Tukur Buratai (ritaya), ya bayyana kasuwar Jilli da ke kan iyakar Borno da Yobe a matsayin “cibiyar hadahadar kayan ta’addanci”, inda ya ce tun da daɗewa ’yan ta’adda ke amfani da wurin wajen tara haraji da samun kayan abinci da makamai.
Buratai ya yi wannan bayani ne a ranar Lahadi, inda ya kare harin bam da Rundunar Sojin Sama ta kai a kasuwar, yana mai cewa aikin soja ne da aka yi bisa sahihin bayanan sirri.
A cewar rahotanni, aƙalla mutane 56, mafi yawansu ’yan kasuwa, ake zargin sun mutu yayin da wasu 14 ke jinya sakamakon harin da aka kai a ranar Asabar.
Rundunar Sojin Sama ta ce ta fara bincike kan lamarin, tana mai jaddada cewa tana ɗaukar duk wani rahoton da ya shafi fararen hula da muhimmanci da tausayi.
- Sojoji ta fara binciken harin bam a Kasuwar Jilli
- Harin Sama: Mun rufe kasuwar Jilli shekaru 5 da suka wuce — Zulum
Sai dai Buratai ya ce harin ba na kuskure a ba ne, illa dai aikin soja da aka yi bisa bayanan sirri da suka nuna cewa ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP na amfani da kasuwar wajen tara haraji, sayen kaya da kuma shirya hare-hare.
Ya ƙara da cewa a shekarar 2018, lokacin da aka gudanar da Operation LAST HOLD, sojoji sun mamaye yankin tare da kai hare-hare kan ’yan ta’adda a kokarin rushe cibiyoyinsu.
Ya ci gaba da cewa, duk da cewa an sha rufe kasuwar, amma ’yan ta’adda suna ci gaba da amfani da ita tare da goyon bayan wasu da ke cinikayya da su.
Buratai ya bayyana cewa duk da cewa rasa rayukan fararen hula abin baƙin ciki ne, laifin ya rataya a kan ’yan ta’adda da ke fakewa da jama’a a matsayin garkuwa. Y
a yi kira ga al’ummomin Geidam, Gubio, Damasak da Ngamdu da su guji cinikayya a kasuwannin da ’yan ta’adda ke amfani da su.
Ya yi addu’ar samun rahama ga waɗanda suka mutu a lamarin tare da fatan samun sauƙi ga wadanda suka jikkata, yana mai jaddada cewa nasara kan ta’addanci za ta tabbata idan sojoji da al’umma suka haɗa kai.