Konate zai sabunta kwantaraginsa a Liverpool

A baya rahotanni sun riƙa cewa Konate zai koma Real Madrid kyauta a ƙarshen kakar nan.

Konate zai sabunta kwantaraginsa a Liverpool

Ɗan wasan baya na Faransa, Ibrahima Konate, ya bayyana cewa yana dab da cimma yarjejeniya da Liverpool domin tsawaita zamansa a ƙungiyar har bayan kakar wasa ta bana.

Konate, mai shekaru 26, yana cikin watannin ƙarshe na kwantiraginsa, inda a baya rahotanni suka riƙa cewa zai koma Real Madrid kyauta.

Sai dai wannan zance ya lafa bayan fara kakar wasan bana da ƙafar hagu, inda a yanzu ake sa ran zai ci gaba da zama a Anfield.

“Mun daɗe muna tattaunawa da ƙungiyar, kuma yanzu mun kusa da cimma matsaya,” in ji Konaté bayan nasarar da Liverpool ta samu 2-1 a wasan hamayya da Everton.

Ya ƙara da cewa akwai yiwuwar zai ci gaba da zama a ƙungiyar a kakar wasa mai zuwa, yana mai jaddada cewa hakan shi ne abin da yake fata tun farko.

A farkon wannan shekara, Konaté bai haska a wasu wasanni uku ba a sakamakon rasuwar mahaifinsa, amma ya dawo cikin gaggawa domin taimakawa ƙungiyar a lokacin da take fama da ‘yan wasa masu jinya.

Duk da cewa Liverpool ta lashe gasar Premier League a bara ƙarƙashin jagorancin koci Arne Slot, amma kakar bana ba ta yi wa ƙungiyar yadda aka zata ba, inda ta soma da jimamin rasuwar ɗan wasa Diogo Jota.