Kotu ta dakatar da sayar da filin FGC Kano

Kotun ta ce a dakata da komai har lokacin da za ta yanke hukuncin ƙarshe.

Kotu ta dakatar da sayar da filin FGC Kano

Babbar Kotun Jihar Kano, ta bayar da umarnin dakatar da gini a wani fili mai faɗin hekta 30 na Kwalejin Gwamnatin Tarayya (FGC) Kano.

Alƙali Yusuf Ubale Muhammad ne, ya bayar da wannan umarni a ranar Laraba, bayan buƙatar da tsofaffin ɗaliban makarantar (FGCKOSA) suka shigar.

Shari’ar ta shafi Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, hukumomin ƙasa na Kano, da kuma wani kamfanin gine-gine mai zaman kansa.

Ƙungiyar tsofaffin ɗaliban na ƙalubalantar yarjejeniyar Naira biliyan takwas da aka bai wa kamfanin Pluck Global Construction Company, kan hakan na iya lalata martabar makarantar.

Kotun ta umarci dukkanin ɓangarorin da su ci gaba da kasancewa yadda abubuwa suke, tare da hana yin duk wani gini a filin makarantar har sai an yanke hukunci.

Makarantar kan titin zuwa Zariya, kusa da Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano, kuma an ƙiyasta darajarsa ta haura Naira biliyan 30, wanda hakan ya sa yake da muhimmanci sosai.

Kotun ta kuma amince a miƙa wannan umarni ga Ministan Ilimi da ke Abuja ta hanyar kamfanin DHL.

An ɗage shari’ar zuwa ranar 14 ga watan Mayu, 2026.

Ƙungiyar FGCKOSA ta buƙaci Shugaban Ƙasa Bola Tinubu da ya sa baki, tana mai cewa filin na daga cikin tarihin makarantar.

Yayin da Ma’aikatar Ilimi ke cewa aikin zai kawo sabbin gine-gine da gyare-gyare, masu ƙara sun bayyana cewa an rage wa filin daraja.

Gwamnatin Jihar Kano ta ce ba ta da hannu a lamarin, tana jaddada cewa filin mallakin Gwamnatin Tarayya ne.