Kotu ta hana INEC amincewa da duk wani taro da ADC tsagin David Mark zai shirya
Kotun ta dakatar da David Mark da sauran shugabbanin jam’iyyar daga shiga ayyukan zaɓɓaɓun shugabannin jam’iyyar.
(Hoto: us.fotolia.com)
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta hana Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), amincewa da ma halartar duk wani taro da ADC tsagin David Mark zai shirya.
Alƙalin da ta yanke hukuncin, Mai shari’a Joyce Abdulmalik ta kuma dakatar da David Mark da sauran shugabbanin jam’iyyar daga shiga ayyukan zaɓɓaɓun shugabannin jam’iyyar a faɗin jihohi.
- Sojoji sun yi nasarar hallaka ’yan ta’adda 11 a Yobe
- Cikin ɗalibai 10 na jami’o’in Najeriya 6 suna harkar damfara ta yanar gizo — EFCC
Haka zalika ta hana INEC ɗin amincewa da babban taron ADC na ƙasa da ta gudanar a baya-bayan nan.
Aminiya ta rawaito cewa hukuncin ya biyo bayan ƙarar da Norman Obinna da ƙarin wasu mutum shida suka shigar a madadin shugabanni da masu zartaswar jam’iyyar.
Masu ƙarar sun ƙalubalanci halascin matakin da shugabannin riƙo na ƙasa suka ɗauka, musamman batun zaɓen jihohi ta hannun kwamitin da suka samar.
Masu ƙarar sun musanta cewa shugabannin riƙon ba su da dama a dokar ƙasa wajen shirya zaɓuka ko ma naɗa kwamitin da za su yi hakan.