Kotu ta soke zaben dan majalisar NNPP a Kano
An soke zaben ne saboda badakalar takardun karatu
Kotun sauraron kararrakin zabe a a Jihar Kano ta soke nasarar da dan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar Tarauni, Mukhtar Yarima na jam’iyyar NNPP ya samu.
Kotun, wacce ke sauraron kararrakin zaben ’yan majalisun jihohi da na tarayya ta yanke hukuncin ne yayin zamanta na ranar Alhamis.
- ECOWAS ta fara sabon taro kan daukar matakin soji a Nijar
- An kashe dan takarar shugaban kasa a taron yarikin nema zaben
Kotun dai ta ce ta soke zaben ne saboda zargin badakakar takardun karatun dan majalisar.
Dan takarar jam’iyyar APC, kuma tsohon dan majalisar mazabar, Hafizu Kawu ne ya kai karar yana kalubalantar sahihancin takardun na Yarima.
Alkalan kotun guda uku da ke karkasjin jagorancin Mai Shari’a I.P. Chima, ta ce Yarima bai cancanci tsayawa takara ba saboda ya gabatar da sakamakon kammala Firamare ta bogi.
Kotun ta ce dan takarar na APC ya yi kokarin gamsar da kotun da isassun hujjoji cewa takardun da dan takarar ya gabatar na bogi ne.
Daga nan ne kotun ta ce NNPP ba ta da dan takara a zaben, don haka duk kuri’un da ya samu sun zama na banza.
Kotun ta kuma bukaci Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), da ta janye takardar shaidar lashe zaben da ta ba dan majalisar na NNPP.
Ta kuma ce shaidar da ya bayar cewa ya canza sunansa zuwa suna uku (Umar Mukhtar Zakari) a shekara ta 2022 ba ta wadata ba, saboda fasfo dinsa na tafiye-tafiye suna biyu yake dauke da shi tun shekara ta 2009 na dauke da suna biyu (Umar Mukhtar).
Kazalika, kotun ta ce hatta takardar kammala firamaren Hausawa da ke Kano da dan majalisar ya gabatar ba ta inganta ba, saboda makarantar ma ta nesanta kanta daga takardar.