Kotun Koli ta tabbatar da David Mark a matsayin Shugaban Jam’iyyar ADC
Wannan hukunci ya maida shugabancin da David Mark ke jagoranta kan madafun iko, bayan da Hukumar Zaɓe mai zaman kanta (INEC) ta soke sunayensu a baya.
Kotun Ƙoli ta soke umarnin nan na “status quo ante bellum” (dawo da komai yadda yake a da) wanda Kotun Daukaka Kara da ke Abuja ta bayar game da rikicin shugabancin Jam’iyyar ADC.
Wannan hukunci ya dawo da shugabancin da David Mark ke jagoranta kan madafun iko, bayan da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta soke sunayensu a baya.
A cikin hukuncin da Alkalan kotun guda biyar suka yanke baki daya a ranar Alhamis, karkashin jagorancin Mai Shari’a Mohammed Lawal Garba, kotun ta bayyana cewa umarnin da kotun ɗaukaka ƙara ta bayar ba shi da muhimmanci.
Haka zalika, kotun ƙolin ta bayyana cewa an shigar da ƙarar kan batun “ikon shari’a” ne bisa wani umarni na musamman ba tare da neman izini daga kotun ɗaukaka ƙara ba tun da fari.