Kotun Koli ta soke taron PDP na Ibadan ta kori Shugabancin Turaki
Alkalan Kotun Kolin sun soki tsagin Kabiru Tanimu Turaki na jam’iyyar game da sake shigar da kara a wata kotu mai daraja daidai da wadda ta bayar da umarnin, domin samun umarni mai karo da na farko, maimakon zuwa Kotun Daukaka Kara
Kotun Kolin Najeriya (Hoto: Onyekachukwi Obi)
Kotun Koli ta soke Babban Taron Kasa na Jam’iyyar PDP da aka gudanar a birnin Ibadan, tare da rushe Shugabancin Jam’iyyar karkashin jagorancin Kabiru Tanimu Turaki, da aka zaba a taron.
A yayin da take yanke hukuncin, wanda ya samu rinjayen mutum uku cikin alkalai biyar, Kotun Koli ta bayyana cewa daukaka karar da Tsagin Tanimu Turaki na Jam’iyyar PDP ba shi da hujja, don haka suka yi watsi da shi.
Tsagin Kabiru Tanimu Turaki ya daukaka kara zuwa Kotun Koli ne domin neman a soke hukuncin Kotun Daukaka Kara wadda ta tabbatar da hukuncin Babbar Kotun Tarayya, Nyesom Wike, da ta soke Babban Taron da jam’iyyar ta gudanar a Ibadan, hukuncin da ya hana Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) amincewa da duk abin da taron ya haifar.
Idan ba a manta ba, Tsagin Wike na PDP ne ya shigar da kara domin kalubalantar halascin taron na Ibadan, wanda a lokacin taron ne aka zabi shugabancin Turaki tare da korar Wike da wasu kusoshin jam’iyyar, sakamakon rikicin shugabanci da ya jima yana dabaibaye jam’iyyar.
Da yake karanta hukuncin kotun a ranar Alhamis, Mai Shari’a Stephen Adah, ya bayyana cewa alkalai ukun da suka yi rinjaye sun bayyana cewa taron da tsagin Turaki na Jam’iyyar ya gudanar a ranar 15 da 16 ga watan Nuwamba ya saba da umarnin Mai Shari’a James Omotosho na Babbar Kotun Tarayya da kuma hukuncin Kotun Daukaka Kara da suka hana gudanar da taron.
Daga nan suka soke daukaka karar da tsagin na Turaki ya shigar, inda suke takaddama da bangaren Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyeson Wike, kan shugabancin Jam’iyyar.
Alkalan Kotun Kolin sun soki tsagin Kabiru Tanimu Turaki na jam’iyyar game da sake shigar da kara a wata kotu mai daraja daidai da wadda ta bayar da umarnin, domin samun umarni mai karo da na farko, maimakon zuwa Kotun Daukaka Kara. Sun bayyana matakin a matsayin wasa da tsarin shari’a, tare da cewa duk mai shigar da kara da ya kuskura saba wa tsarin kotu, ya kuka da kansa.
Alkalan Kotun Kolin sun bayyana cewa duk da cewa rikici da harkokin cikin gidan jam’iyya abu ne da ya kebance ta, amma wajibi ne ya kasance a yi komai bisa kundin tsarin mulki da dokar zabe, da umarnin kotu kan al’amurin babban taro da sauransu.