Kwamishinan El-Rufai ya shiga takarar Gwamna a Jam’iyyar ADC

Sani ya yi aiki a matsayin Kwamishinan Ma’aikatar ƙaramar Hukuma da Masarautu, sannan daga baya ya zama Kwamishinan Ilimi a zamanin mulkin El-Rufai.

Kwamishinan El-Rufai ya shiga takarar Gwamna a Jam’iyyar ADC

Malam Jafaru Ibrahim Sani, ɗaya daga cikin tsofaffin Kwamishinoni a gwamnatin Malam Nasir El-Rufai, tsohon gwamnan jihar Kaduna, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamna a ƙarƙashin jam’iyyar ADC.

Sani ya yi aiki a matsayin Kwamishinan Ma’aikatar ƙaramar Hukuma da Masarautu, sannan daga baya ya zama Kwamishinan Ilimi a zamanin mulkin El-Rufai.

Tuni dai Malam Sani ya sayi fom domin neman wannan babban matsayi na Gwamnan jihar.

Wakilinmu ya tuntuɓe shi ta kafar WhatsApp, inda ya tabbatar da wannan shawara tasa ta hanyar wani gajeren saƙo.

“Muna ƙoƙarin kasancewa cikin masu neman takara. Allah Ya yi mana jagora,” in ji shi a taƙaice.

A ranar Laraba ne aka hango shi tare da sauran masu neman takarar Gwamna da suka halarci wani taro, inda suka amince su yi aiki tare domin tabbatar da nasarar jam’iyyar ADC a zaɓen shekarar 2027.

Sauran masu neman takarar gwamna a ƙarƙashin jam’iyyar ta ADC sun haɗa da tsohon ɗan takarar Gwamna na jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, Isah Ashiru Kudan da Farfesa Muhammad Sani Bello da Shuaibu Idris Mikati, da kuma Tijjani Ahmad.