Ma’aikaci ya rasu a hanyarsa ta zuwa aiki a Abuja

An tabbatar da rasuwar ma’aikacin bayan kai shi Asibitin Koyarwa na Gwagwalada.

Ma’aikaci ya rasu a hanyarsa ta zuwa aiki a Abuja

Taswirar Babban Birnin Tarayya Abuja

Wani ma’aikaci mai goge-goge a ofishin Ƙungiyar Malamai ta Ƙasa reshen Abuja (FCT NUT), Jessey A. Audu, ya rasu a hanyarsa ta zuwa aiki da safe.

Wani ma’aikacin Ƙungiyar Ibrahim Adamu, ya ce lamarin ya faru ne bayan marigayin, ya bar gida, inda ya yanke jiki ya faɗa wani rami da misalin ƙarfe 11 na safe.

Daga nan ne  waɗanda suka gano gawar tasa suka sanar da ofishin ‘yan sanda, su kuma suka kira ofishin NUT, bayan wasu masu wucewa sun bayyana wane ne shi.

Tuni dai NUT ta miƙa shi Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abuja da ke Gwagwalada, inda aka tabbatar da rasuwarsa.

Margayin dai ɗan asalin garin Yelwa ne da ke Ƙaramar Hukumar Toto a Jihar Nasarawa, amma yana zaune ne a Unguwar Dodo da ke Gwagwalada.

Ya rasu ya bar mata guda ɗaya, da yara biyu.