Magidanci ya sari matarsa da adda har lahira

Al’ummar yankin sun nemi su halaka mutumin saboda saran matar tasa da ya yi da adda a kanta, har ta rasu

Magidanci ya sari matarsa da adda har lahira

’Yan sanda. (Hoto: NAN)

’Yan sanda sun cika hannu da wani magidanci bayan da ya sari matarsa da adda a kai, ta ce ga garinku nan.

’Yan sanda sun kama magidancin ne bayan samun rahoton aika-aikan da ya yi wa mai dakin tasa a sakamakon takaddamar da suka samu a tsakaninsu.

Lamarin ya faru ne a sabuwar unguwar Upper Mission da ke garin Benin, hedikwatar Jihar Edo.

Kakakin ’yan sandan jihar, CSP Moses Yamu, ya ce ko da ’yan sanda daga babban ofishinsu da ke yankin Aduwawa suka isa wurin, sun iske matar kwance cikin jini, da mummunan sara a kanta.

Ya ce, al’ummar yankin sun nemi su halaka shi saboda saran matar tasa da ya yi da makami, amma ya sha da kyar.

Ya bayyana cewa da kyar ’yan sanda suka kwaci mutumin daga hannun jama’a, suka tafi da shi domin tsarewa da kuma yi masa tambayoyi.

CSP Moses Yamu ya ce ’yan sanda sun kai matar asibiti inda likita ya shaida musu cewa rai ya riga ya yi halinsa.

Jami’in ya kara da cewa Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Edo, Betty Otimenyin, ya koka bisa yadda ake samu karuwar fada da makami a tsakanin ma’aurata a jihar.

Daga nan ya ba da umarnin a gudanar da zuzzurfan bincike kan lamarin domin hukunta mai laifi yadda doka ta tanadar.

Dan kwallon Najeriya ya mutu bayan fadowa daga bene a Uganda

Luwadi: Magijanci ya lalata dan shekara 5 a Zariya

Magidanci ya sari matarsa da adda har lahira

Ya daɓa wa yayansa wuƙa saboda Naira 700