Mahaifiyar tsohon Gwamnan Borno Ali Modu Sheriff ta rasu

Za a yi jana’izar mahaifiyar tsohon Gwamnan Borno Ali Modu Sheriff ranar Litinin 1 ga Yuli, 2024

Mahaifiyar tsohon Gwamnan Borno Ali Modu Sheriff ta rasu

Mahaifiyar tsohon Gwamnan Jihar Borno, Sanata Ali Modu Sheriff ta riga mu Gidan Gaskiya.

Mahaifiyar tsohon gwamnan, Hajja Aisa, ta koma ta Mahaliccinta ne a ranar Lahadi a Maiduguri, babban birnin jihar.

Ta rasu tana da shekaru 93, bayan fana da rashin lafiya.

Sanarwar rasuwar ta bayyana cewa za yi jana’izar Hajja Aisa da Azahar ranar Litinin 1 ga watan Yuli, 2024.

Za a yi jana’izar ne a gidant Marigayi Galadima Modu Sheriff d da ke Damboa Road a Maiduguri.

Sanarwar ta kuma roka wa marigayiyar gafara da kuma Aljannatul Firdaus.