Majalisa ta amince da Murtala Garo a matsayin Mataimakin Gwamnan Kano

Majalisar ta tabbatar da zabin Murtala Garo ne kasa da mako guda bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya aike mata ta bukatar hakan.

Majalisa ta amince da Murtala Garo a matsayin Mataimakin Gwamnan Kano

Majalisasr Dokokin Jihar Kano ta tabbatar da zabin Murtala Sule Garo a matsayin sabon mataimakin gwamnan jihar.

Majalisar ta tabbatar da zabin Murtala Garo ne a yayin zamanta na ranar Litinin, kasa da mako bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya aike mata ta bukatar hakan.

Amincewar ta biyo bayan gabatar da rahoton kwamitin wucin gwadi da majalisar ta kafa don tantance Garo, karkashin jagorancin Mataimakin Shugaban Majalisar, Muhammad Bello.

Gwamnan Abba ya aike da sunan Murtala Sule Garo ne, bayan gibin da aka samu, sakamakon murabus din da tsohon mataimakinsa, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya yi.

Kwamitin ya bayyana cewa an yi wa Garo zuzzurfan tantancewa da suka danganci tambayoyi kan ayyukansa na baya, karatunsa, kwarewarsa da kuma fahimtar shugabanci da manufar jihar, gami da tantance takardun shaidar karatunsa.

A cewar kwamitin, Garo ya nuna alamar fahimtar nauyin aikin da za a ba shi da manufar jihar kuma ya nuna alamar shirinsa na mara wa Gwamna Abba baya domin sauke nauyin al’ummar jihar da ke kansa.

Sakamakon haka kwamitin ya ba da shawarar amincewa da nadinsa a matsayin sabon mataimakin gwamna, kuma zauren majalisar ya amince da hakan, bisa jagorancin Shugaban Majalisar, Falgore.