Majalisar Jigawa ta ba da umarnin a binciki gwamnatin Badaru

Majalisar ta ce dole ne ta gano yadda aka kashe kuɗaɗen al’umma.

Majalisar Jigawa ta ba da umarnin a binciki gwamnatin Badaru

Gwamnan Jigawa, Mohammad Badaru Abubakar

Majalisar Dokokin Jihar Jigawa, ta bayar da umarnin a binciki tare da ƙwato wasu kuɗaɗe da aka gano akwai matsala a kansu a lokacin mulkin tsohon gwamnan jihar, Muhammad Badaru Abubakar.

Wannan mataki ya biyo bayan amincewa da rahoton Kwamitin Asusun Jama’a na Majalisar, wanda ya binciki yadda ma’aikatu, hukumomin gwamnati da ƙananan hukumomi 27 na jihar suka kashe kuɗaɗen gwamnati.

Shugaban kwamitin, Hon. Isyaku Abubakar, ya ce binciken ya samo asali ne daga rahotannin Babban Mai Binciken Kuɗi na Jihar da na ƙananan hukumomi, tare da sauraron bayanai daga manyan jami’an gwamnati.

Ya ce an gayyaci kwamishinoni, sakatarori, daraktocin kuɗi da shugabannin ƙananan hukumomi domin su yi bayani kan wasu kuɗaɗe da ake zargin sun yi ɓatan-dabo.

Rahoton, ya nuna matsaloli kamar rashin cikakkun takardu, saɓani a kashe kuɗi da kuma rashin ingantaccen sanya ido a wasu hukumomi.

Majalisar ta ce dole ne a ƙwato duk kuɗaɗen da aka gano akwai matsala a kansu, sannan a ɗauki matakin da ya dace.

Haka kuma, ta buƙaci a gyara tsarin aiki, a ƙara horar da ma’aikatan kuɗi, da kuma inganta hanyoyin santa ido domin hana aukuwar irin wannan matsala a gaba.

Shugaban Majalisar, Hon. Haruna Aliyu, ya yaba wa kwamitin bisa aikin da ya yi, yana mai cewa majalisar za ta ci gaba da sa ido domin tabbatar da an yi amfani da dukiyar jama’a yadda ya kamata.

Majalisar, ta ce wannan aiki na daga cikin nauyin da kundin tsarin mulki ya ɗora mata na kula da yadda ake kashe kuɗin gwamnati cikin gaskiya da riƙon amana.