Yadda ambaliya ta mamaye gidaje da shaguna a Jalingo

Ambaliyar ta haifar da tsaikon zirga-zirgar ababen hawa a yankin.

Yadda ambaliya ta mamaye gidaje da shaguna a Jalingo

Gidaje da dama, shaguna da makarantu sun nutse sakamakon ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da aka tafka na sa’o’i a Jalingo, babban birnin Jihar Taraba.

An fara ruwan saman ne da misalin ƙarfe 2:30 na dare kuma ya ci gaba da zuba har wajen ƙarfe 11:30 na safiyar ranar Asabar.

Duk da cewa ruwan ya zama waraka ga mazauna garin bayan makonni da aka shafe ana fuskantar tsananin zafi, sai dai ya yi ɓarna.

Unguwanni kamar Mile Six, Mafindi da Mayogwai su ne suka fi fuskantar ambaliyar.

Haka kuma, Kasuwar Jalingo ta cika da ruwa inda shaguna da dama suka nutse.

Wani mazaunin Mile Six, Bulus James, ya ce gidansa na daga cikin waɗanda ambaliyar ta shafa, inda ya rasa kayan gidansa da muhimman takardunss.

Ya danganta ambaliyar da toshe magudanan ruwa sakamakon zubar da shara ba bisa ƙa’ida ba.

Ya ce mazauna yankin sun yi ƙoƙarin fito da kayayyakinsu yayin da ruwan saman ke sauka, amma yawan ruwan ya hana da yawa daga cikinsu yin hakan.

Haka kuma, an samu tsaikon zirga-zirga daga hanyar Jalingo zuwa Wukari bayan ambaliyar ta lalata gadar da aka gina kusa da rusasshiyar gadar Namnai.

Wannan ne karo na biyu cikin makonni uku da ambaliya ta lalata wannan gada.

Sakamakon haka, dubban matafiya da motoci sun maƙale a ɓangarorin biyu na Kogin Namnai.

Wani mazaunin garin Namnai, Mallam Tanko Saidu, ya shaida wa Aminiya ta wayar tarho cewa har yanzu matafiya da dama suna maƙale.

Ya ƙara da cewa ana ƙoƙarin kawo kwale-kwale daga garuruwan da ke kusa da kogin domin fara jigilar fasinjoji da motoci zuwa ɗaya gefen kogin.

Ya ce, “Muna ƙoƙarin samo kwale-kwale daga Mayoreniyo da sauran garuruwan da ke bakin Kogin Binuwai domin fara jigilar motoci zuwa ɗaya gefen.”