HOTUNA: Manyan ’yan siyasa sun halarci bikin rantsar da sabon Mataimakin Gwamnan Kano
Na karɓi wannan nauyi a matsayin wata dama ta hidima, kuma zan yi aiki tuƙuru domin tallafa wa ci gaban Jihar Kano.
Fitattun ’yan siyasa da sarakunan gargajiya sun halarci bikin rantsar da sabon Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Murtala Sule Garo, wannan Talatar a Fadar Gwamnatin Kano.
Mai Shari’a Dije Abdu Aboki ce ta jagoranci rantsar da sabon mataimakin gwamnan a gaban manyan jami’an gwamnati da ’yan majalisa da sarakunan gargajiya da kuma masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC.
- Hukumar Alhazai ta ayyana ranar soma jigilar maniyyatan Kano
- Harin Boko Haram ya laƙume rayuka 24 a sansanin sojin Chadi
Daga cikin waɗanda suka halarci bikin akwai tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje, da takwaransa, Ibrahim Shekarau, da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, da Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, tare da sauran manyan masu ruwa da tsaki.
Da yake jawabi bayan rantsar da shi, Garo ya miƙa godiyarsa ga gwamnan tare da alƙawarin yi masa biyayya da ba shi cikakken haɗin kai.
“Na karɓi wannan nauyi a matsayin wata dama ta hidima, kuma zan yi aiki tuƙuru domin tallafa wa jagorancin gwamna wajen ci gaban Jihar Kano,” in ji shi.
Ya kuma yaba wa Majalisar Dokokin Jihar Kano bisa amincewa da shi, tare da jaddada aniyarsa ta aiki da manufofi da shirye-shiryen gwamnati domin amfanin al’umma.

A nasa jawabin, Gwamna Yusuf ya bayyana cewa zaɓin Garo a matsayin wani mataki ne na ƙarfafa haɗin kai, tabbatar da ci gaba da kuma samar da daidaito a harkokin mulki.
Ya ce naɗin ya biyo bayan tuntuɓa mai zurfi da masu ruwa da tsaki, tare da la’akari da buƙatar haɗa kowa da kowa da kuma samar da ingantaccen shugabanci.
Ana iya tuna cewa dai, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ɗauki Murtala bayan Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya ajiye muƙaminsa sakamakon dambarwar sauyin sheƙa daga jam’iyyar NNPP zuwa APC.


