Marasa tunani ke zaton ina yi wa Tinubu aiki — Kwankwaso

Yayin wata hira da aka yi da shi a tashar talabijin ta Global TV a daren Laraba, Kwankwaso ya ce wannan jita-jita ta daɗe tana yawo tun lokacin da yake jam’iyyar NNPP.

Marasa tunani ke zaton ina yi wa Tinubu aiki — Kwankwaso

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi watsi da zargin da ake masa na cewa yana aiki a asirce domin taimaka wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Yayin wata hira da aka yi da shi a tashar talabijin ta Global TV a daren Laraba, Kwankwaso ya ce wannan jita-jita ta daɗe tana yawo tun lokacin da yake jam’iyyar NNPP.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito yadda Sanusi Bature, mai magana da yawun Gwamna Abba Yusuf, ya yi zargin cewa Sanata Kwankwaso yana gudanar da wasu tsare-tsare a asirce don ciyar da muradun Tinubu gaba gabanin zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027, lokacin wata hira da aka yi da shi a tashar talabijin ta Arise News a ranar Laraba.

Bature ya ce: “Akwai waɗanda ke aiki tare da Tinubu a bayyane kuma kai-tsaye a idon jama’a, sannan akwai waɗanda za su iya yi masa aiki a bayan fage.

“Na yi amanna cewa, duk abin da Kwankwaso ke yi zai amfani Tinubu ne a ƙarshen lamari, domin Kwankwaso ya yi wa Tinubu aiki a shekarar 2023.

“Ni ɗan jam’iyyar APC ne; na taɓa zama mai magana da yawun jam’iyyar adawa a Kano, kuma na san abin da ya faru a 2023. Na yi amanna Kwankwaso yana yi wa Tinubu aiki na zaɓen 2027 a bayan fage.”

Dangantaka tsakanin Kwankwaso da Gwamna Abba Kabir Yusuf ta yi tsami biyo bayan matakin da gwamnan ya ɗauka na komawa jam’iyyar APC, saɓanin ra’ayin tsohon jagoran nasa na siyasa.

Sai dai yayin da yake mayar da martani kan wannan zargi, Kwankwaso ya ce: “Ina ga mutane marasa tunani ne kawai za su yi amanna da hakan. Mu ba ma yi wa kowa aiki. Mu kawai muna aiki ne domin jam’iyyar NDC.

“Bola Tinubu yayana ne kuma babban abokina ne har zuwa yau. Amma hakan ba yana nufin za mu haɗe dukkan aƙidunmu na siyasa wuri guda da shi ba. Shiga yana yin nasa, ni kuma ina yin nawa.”

Kwankwaso ya ƙara da cewa Shugaba Tinubu ba shi da cikakkiyar masaniya kan matsalolin da ke addabar ƙasar nan saboda mutanen da ke kusa da shi ba sa gaya masa gaskiya.

Ya bayyana cewa: “A al’adance a irin yanayin da ake ciki yanzu, shugaban ƙasa ba zai iya ganin abin da ke faruwa ba. Kuma abin takaici, mafi yawancin mutanen da ke kewaye da shi su ne ma ainihin masu haddasa matsalolin.

“Saboda haka, a irin wannan yanayi, yana da wuya a ga wanda zai ba shi shawara ko ya gaya masa ainihin gaskiyar halin da ake ciki. Abin da suka saba faɗa da abin da suke yi shi ne lalubo gwamnoni. Ina ga idan aka duba yawan gwamnonin da ake da su yanzu, APC ce ta ɗaya.”