Masu ibadar Umarah 42 sun mutu a hatsarin mota a hanyar zuwa Makka
Allah Ya yi wa masu ibadar Umara 42 rasuwa bayan motarsu ta yi taho-mu-gama da wata tankar mai a kasar Saudiyya
Hatsarin alhzan Indiya a Madina
Wasu masu ibadar Umara 42 sun mutu bayan da motarsu ta yi taho-mu-gama da wata tankar mai a kusa da birnin Madina da ke kasar Saudiyya.
Dukkan masu ibadar ’yan kasar Indiya ne, kuma hatsarin ya ritsa da su ne a kan hanyarsu ta zuwa Makka bayan kammala ziyara a birnin Madina.
Ministan harkokin wajen Indiya Dakta S. Jaishankar ya bayyana cewa mutum daya daga cikin fasinjojin ya tsallake rijiya da baya a hatsarin da ya auku da tsakar daren Litinin.
Hatsarin ya auku ne a bayan da motar safa mai daukar mutum 43 da masu ibadar suke ciki ta yi karo gaba-da-gaba da wata tankar mai.
- ’Yan ta’adda sun sace dalibai 25 a dakunan kwanansu a Kebbi
- NELFUND ya raba wa ɗalibai tallafin karatu na Naira Biliyan 116
A sakon ta’azaiyyarsa ga iyalan mamatan, Ministan harkokin wajen Indiya, ya bayyaan cewa ofisoshin jakadancin kasar ke Saudiyya, na bayar da cikakken tallafi ga masu Umarar da hatsarin ya rusta da su.