Masu sauya sheka na iya samun takara a sabbin jam’iyyu
Hukuncin kotun na nufin mutanen da suka sauya sheka bayan sun fadi zaben fid-da-gwani a jam’iyyunsu na iya shiga a dama da su kuma su samu takara a sabbin jam’iyyun da suka koma a zaben 2027.
(Getty Images)
Kotu ta bude wa jam’iyyu damar tsayar da sabbin ’yan takara har zuwa watan Satumbar wannan shekarar ta 2026, da ta soke watsie da jadawalin Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) da ya kayyade gudanar da zaben ’yan takara da mika mata sunayensu zuwa karshen watan nan na Mayu.
Hukuncin kotun na nufin mutanen da suka sauya sheka bayan sun fadi zaben fid-da-gwani a jam’iyyunsu na iya shiga a dama da su kuma su samu takara a sabbin jam’iyyun da suka koma a zaben 2027.
Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta bayyana cewa jadawalin INEC mai wa’adin watan Mayu ya saba da Dokar Zabe ta 2026, kuma INEC ba ta da hurumin kirkirar duk wani jadawalin sabanin abin da Dokar Zabe ta taanda.
Hukuncin kotun na zuwa ne bayan jadawalin da INEC ta fitar ya tilasta jam’iyyu mika mata sunayen mambobinta, bisa wa’adin da ta bayar na ranar 10 ga watan Mayu, a yayin da suke fadi tashin gudanar da zaben fitar da kuma mika mata sunayen ’yan takara kafin cikar wa’adin ranar 31 ga watan na Mayu ta ta bayar.
Jadawalin ya kara da cewa sai an sanar da hukumar kwana 21 kafin zaben fitar da ’yan takarar domin ta samu halarta domin sanya ido.
- Yadda aka gano kogwanni da ’yan kwaya ke sheke ayarsu a Kano
- Matashiya mai koyon tuƙi ta murƙushe yara 3 ’yan gida ɗaya
Kafin wannan hukunci, jadawalin INEC ya jefa jam’iyyun da ke fama da rikicin shugabanci a gaban kotu cikin rashin tabbas game da makomarsu a zaben shekarar 2027.
Kazalika ya rufe kofar sauya sheka da kuma neman takara a sabbin jam’iyyu ga masu neman takara da suka fadi a zaben fid-da-gwani a jam’iyyunsu.
Amma a hukuncin da kotun ta yanke, Mai Shari’a Mohammed Umar, ya ce INEC ba ta hurumin doka na sanya ranar da jam’iyyu za su gudanar da zabukan fitar da ’yan takararsu na zaben 2027 sabanin dokar zabe.
Takardar (CTC) hukuncin da kotun ta yanke kan kara mai lamba FHC/ABJ/CS/517/2016, da Jam’iyyar YP take karar INEC, ta tuna jam’iyyar ta gabatar wa kotun bukatu guda shida, kuma dukkansu kotun ta amsa su.
Lauyan masu karar J. O. Olotu, ya yi zargin cewa INEC ta yi jadawalin da ake takaddama a kansa ne da nufin rufe kofar samun takara ga masu neman takara da suka fadi a zaben fid-da-gwani idan suka sauya sheka zuwa wasu jam’iyyu.