Mata sun rushe shingen binciken sojoji a Filato
Amma masu zanga-zangar sun ce sun dauki matakin kona shi ne saboda sun gaji da yawan hare-haren da ake kai musu ba tare da sun samu kariya ba.
Wasu fusatattun mata a yankin Gashish sun tarwata shingen bincike da sojoji suka kafa a kusa da yankin Kassa da ke Karamar Hukumar Barkin Ladi a Jihar Filato a ranar Litinin.
Shingen binciken, wanda dakarun Operation Enduring Peace suka kafa, an yi shi ne domin tabbatar da tsaro a kan hanyar da ke bi ta yankin.
Amma masu zanga-zangar sun ce sun dauki matakin kona shi ne saboda sun gaji da yawan hare-haren da ake kai musu ba tare da sun samu kariya ba.
Matan sun yi boren ne bayan harin da ’yan bindiga suka kai a daren Lahadi a kauyen Hurum-Gashish, inda aka kashe mutane hudu, aka jikkata wasu biyar.
- An ci zarafin yara 205 a Gombe a wata 10
- DAGA LARABA: Shin kare kai daga harin ’yan ta’adda zai kawo karshen matsalar tsaro?
A wani hari na daban a kauyen Bachi kuma, an kashe mutane biyu, yayin da wasu da dama suka jikkata.
Matan sun bayyana cewa duk da kasancewar jami’an tsaro a yankin, amma ba a daina kawo wa al’ummar hare-hare ba.
Daya daga cikin matan mai suna Mercy Dachung ta ce, “Mun gaji da binne ’ya’yanmu da mazajenmu. Sojoji suna nan a wurin, amma har yanzu ana kashe mu. Idan ba za su kare mu ba, su tafi kawai.”
Ita ma Nancy Gyang ta ce jami’an tsaro sukan iso ne bayan an gama kai hare-haren. “Mun rushe shingen tsaron saboda bai hana kashe-kashen ba,” in ji ta.
Shugaban al’umma, Chundung Bot, ya ce jama’a ba su da kwarin gwiwa kan jami’an tsaro, inda ya bukaci gwamnati da hukumomin da abin ya shafa su dauki matakan gaggawa domin dawo da zaman lafiya.