Mataimakin shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilai ya fice daga PDP

Ya bayyana rikicin cikin gida a matsayin dalilin yanke wannan hukunci.

Mataimakin shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilai ya fice daga PDP

Mataimakin Shugaban Marasa Rinjaye a Majalisar Wakilai, Ali Isa JC, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP.

Ya bayyana rikicin cikin gida da rashin bin tsarin dimokuraɗiyya a matsayin dalilin da suka sanya shi ficewa daga jami’yyar.

Wannan na cikin wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan watan 14 ga watan Afrilun 2026, wadda ya aike wa shugaban gundumar Kindiyo da ke Ƙaramar Hukumar Balanga a Jihar Gombe.

Ali Isa, wanda ke wakiltar mazaɓar Balanga/Billiri, ya bayyana cewa ya yanke wannan shawarar ne, bayan ya tattauna da iyalansa, abokan siyasarsa, da kuma masu ruwa da tsaki a mazaɓarsa.

Ya koka da cewa jam’iyyar PDP ta kauce wa tsofaffin manufofinta, inda ya zargi wasu tsiraru da karɓe ragamar shugabancin jam’iyyar domin biyan buƙatunsu.

“Na ɗauki wannan mataki ne sakamakon yadda wasu marasa kishin dimokuraɗiyya suka ƙwace jam’iyyar, lamarin da ya haifar da rarrabuwar kai da shugabanci na ɓangaranci, wanda hakan ya saɓa wa muradun da aka kafa jam’iyyar tun farko,” in ji shi.

Kodayake ɗan majalisar bai bayyana sunan jam’iyyar da zai koma ba.

Amma ya jaddada cewa matakinsa na gaba zai ginu ne kan wani dandamali da zai ba shi damar ci gaba da yi wa al’ummar Balanga da Billiri hidima yadda ya kamata.

Ya ƙara da cewa mazaɓarsa na buƙatar dandalin siyasa mai tabbas da kwanciyar hankali wanda zai kare muradunsu.

Ɗan majalisar ya nuna godiyarsa ga jam’iyyar PDP bisa damar da ta ba shi na wakiltar jama’arsa a matakin ƙasa.