Matsalar tsaro na gurgunta tattalin arzikin Najeriya — Tinubu

Tinubu ya ce ƙarfafa tsaro muhimmin ginshiƙi ne wajen cimma manufofinsa na Sabunta Fata na  ‘Renewed Hope Agenda’.

Matsalar tsaro na gurgunta tattalin arzikin Najeriya — Tinubu

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce matsalar tsaro da ke addabar kusan dukkan sassan Najeriya na ci gaba da hana bunƙasar tattalin arzikin ƙasar.

Tinubu ya tabbatar wa ’yan ƙasa cewa gwamnatinsa za ta ɗauki tsauraran matakai don murƙushe ’yan ta’adda da ’yan fashin daji da ke hana ruwa gudu a ƙasar.

Shugaban ya bayar da wannan tabbacin ne yayin jawabi a taron Majalisar Tattalin Arziki ta Ƙasa (NEC) a Abuja, inda ya ce rashin tsaro na hana zaman lafiya da ci gaban ƙasa.

Ya jaddada aniyar ƙarfafa jami’an tsaro domin kawar da ta’addanci, yana mai cewa ayyukan ’yan bindiga ba su cikin al’adun Najeriya.

Shugaban ya kuma yaba wa gwamnonin wasu jihohi, musamman Borno, Kaduna da Katsina, dangane da ƙoƙarinsu wajen yaƙi da rashin tsaro, tare da cewa Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da aiki da jihohi don kare rayuka da dukiyoyin al’ummar ƙasar.

Haka kuma Tinubu ya ce ƙarfafa tsaro muhimmin ginshiƙi ne wajen cimma manufofinsa na Sabunta Fata na  ‘Renewed Hope Agenda’, yana mai bayyana cewa sauye-sauyen tattalin arziki da manufofin kuɗi sun fara haifar da sakamako mai kyau, tare da dawo da ƙwarin gwiwar masu zuba jari.