MTN ya dakatar da tsarin rancen katin waya da data

Tsarin Xtratime yana bai wa kwastomomi da ke kan tsarin prepaid damar aron katin kiran waya ko data, sannan su biya bayan sun sake sayen katin kiran waya ko data

MTN ya dakatar da tsarin rancen katin waya da data

Kamfanin MTN

Kamfanin sadarwa na MTN Nigeria ya ba da sanarwar da dakatar da tsarinsa na rancen katin kiran waya da data da ake kira Xtratime.

Kamfanin ya dakatar da tsarin ne sakamakon sabbin ƙa’idojin da Hukumar Kare Gasa da Kare Masu Amfani (FCCPC) ta gabatar.

“MTN Nigeria na sanar da Nigerian Exchange Limited da masu zuba jari cewa ya dakatar da tsarin rancen kiran waya da na data (‘Xtratime’) na wucin gadi,” in ji sanarwar da sakataren kamfanin, Uto Ukpanah, ya aike wa kamfanin hadahadar hannun jari na kasa, NGX a ranar  Alhamis

Kamfanin ya ce dakatarwar na da nufin bin sabbin ƙa’idojin da aka kafa a ƙarƙashin dakar bayar da rancen ta hanyoyin zamani na shekarar 2025.

Tsarin Xtratime yana bai wa kwastomomi da ke kan tsarin prepaid damar aron katin kiran waya ko data, sannan su biya bayan sun sake sayen katin kiran waya ko data.

Sanarwar ta bayyana cewa tsarin Xtratime ya faɗa ƙarƙashin sabbin ƙa’idojin da ke buƙatar lasisi na musamman da kuma bin wasu tsare-tsare na doka ga masu bayar da rance ta hanyoyin zamani.

Ta ƙara da cewa dakatarwar na da alaƙa da aiwatar da sabbin tsare-tsare da aka kafa a ƙarƙashin ƙa’idojin 2025, waɗanda suka gabatar da sabon tsarin bin doka da lasisi ga dukkan masu ba da rancen dijital ko na al’ada.

Duk da dakatarwar, MTN ya ce abokan cinikinsa za su ci gaba da samun damar siyan katin kiran waya da data ta sauran hanyoyi, kuma ta jaddada cewa wannan mataki ba zai yi tasiri sosai ga ribar kamfanin ba.

Sabbin ƙa’idojin FCCPC na 2025 sun faɗaɗa ikon kulawa da rancen dijital zuwa kamfanonin sadarwa da sauran masu ba da rance na gajeren lokaci.

Tsarin ya shafi dukkan kamfanonin da ke ba da rancen kiran waya da data  dole ne su yi rajista kuma su samu amincewa kafin su ci gaba da aiki.

Hukumar ta fara gabatar da tsarin kula da rancen dijital tun a 2022, amma ta faɗaɗa shi tare da ƙa’idoji masu tsauri a 2025.

An kafa wa’adin bin doka na wucin gadi, inda ake sa ran cikakken rajista kafin Afrilu 2026.

Ƙara tsaurara ƙa’idojin na nuna damuwa da ƙara yawan basussuka, tsaron bayanai da kuma yadda ake gudanar da rancen dijital da ke ƙara faɗaɗa a Najeriya.