Sakamakon zaben bogi ya tayar da kura a Kogi

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ce tana bincike don gano ta inda wani jabun sakamakon zaben Gwamnan Jihar Kogi da aka gani ya samo asali.

Wata kungiyar fararen hula, YIAGA Africa, ce ta daga kara game jabun sakamakon zaben da ta gani a yayin da ake tsaka da jefa kuri’ar zaben gwamnan jihar Kogi a akwatin zabe mai lamba 004 a mazabar Ogori/Mangogo da ke jihar.

Yadda ake sayen kuri’u a Zaben Gwamnan Kogi

’Yan daba sun bude wa masu zabe wuta a Bayelsa

A sakamakon zaben da aka cike, Jam’iyyar APC mai mulkin jihar ta samu kuri’u 200, ADC, PDP da SPD kowannensu na da kuri’a biyu sai AA mai kuri’a daya.

Dan takarar gwamnan jihar a PDP, Sanata Dino Melaye, ya bukaci wakilan jam’iyyarsa da su yi bore, muddin INEC ta ki nuna masu takardar rubuta sakamakon zaben da ba a rubuta komai a ciki.

A cewarsa, an gaza fara zabe rumfar yadda aka tsara saboda jami’an INEC sun ki nuna wa wakilan jam’iyyarsa takardar rubuta sakamakon zabe da babu komai a ciki.

Sakamakon zaben bogi ya tayar da kura a Kogi

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ce tana inda wani jabun sakamakon zaben Gwamnan Jihar Kogi da aka gani ya samo asali.