Muna goyon bayan a rantsar da Tinubu —Tsagin Jam’iyyar LP

An samu baraka a Jam’iyyar LP da ke kalubalantar nasarar Tinubu a gaban kotu

Muna goyon bayan a rantsar da Tinubu —Tsagin Jam’iyyar LP

Tsagin jam’iyyar adawa ta LP ya bayyana goyon bayansa ga rantsar shugaban kasa mai jiran gado, Bola Tinubu a ranar 29 ga watan Mayu da muke ciki.

Tsagin jam’iyyar, ya kuma zargin dan takarar shugaban kasan jam’iyyar, Peter Obi, da gabatar da bukatar — dakatar da rantsar da Tinubu, wadda bukata ce — da ta  ci karo da kundin tsarin mulkin Najeriya.

An samu baraka a jam’iyyar da ke kalubalantar nasarar Tinubu a gaban kotu ne, bayan jam’iyyar ta bukaci a dakatar da rantsar da Tinubu sai bayan kotu ta yanke hukunci.

Kazalika takaddamar da ta biyo bayan kalaman Archbishop John Onaiyekan wanda ya bukaci kotu ta gaggauta yanke hukunci kan shari’ar kafin  a rantsar da sabon shugaban kasa.

Amma tsagi jam’iyyar ya ce kundin tsarin mulkin Najeriya bai ba da damar samun gibi a kujerar shugaban kasa ba, don haka suka goyi bayan rantsar da Sanata Tinubu, kamar yadda doka ta tanada.

A sanarwar dabangaren LP da Lamidi ke jagoranta ya bayyana cewa rantsar da Tinubu ba zai shafi shari’ar da ke gaban kotu ba.

Hakazalika, idan kotu ta soke nasararsa, kundin tsarin mulki ya riga ya tanadi abin da za a yi.

A cewarsu, “shi kansa Peter Obi ya ci gajiyar irin haka a baya, inda aka rantsar da shi a matsayin zababben gwamna duk da cewa Andy Uba ya shigar da kara a gaban kotu yana kalubalantar nasarar Obi, Don haka abin da yake nema yanzu ya saba doka.”

Amma a martanin kakakin jam’iyyar LP na kasa Obiora Ifoh ya fitar ya zargin shugannin bangaren da zama masu fuska biyu da suka shigo jam’iyyar da nufin su rusa ta.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos