Mutum 19 sun rasu a hatsarin mota a Edo da Taraba
An binne wasu da suka rasu, yayin da aka kai gawarwakin ragowar zuwa asibiti.
Akalla mutum 19 ne suka rasu, yayin da wasu da dama suka jikkata a wasu hadurran mota guda biyu da suka auku a Jihohin Edo da Taraba.
A Jihar Taraba, mutum bakwai ciki har da yara biyu da mata biyu ne, suka rasa rayukansu a wani hatsari da ya auku a ranar Talata da misalin ƙarfe 4 na yamma a yankin Garbabi da ke Karamar Hukumar Gashaka.
- Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 30 a kusa da tafkin Chadi
- An gano ƙarin mutum 10 masu ɗauke da alamomin COVID-19 a Kuros Riba
Hatsarin ya hada da wata motar haya da ke ɗauke da fasinjoji 11 daga Bali zuwa Serti, hedikwatar Karamar Hukumar Gashaka.
Haruna Lukman, wani jami’i na ƙungiyar Motocin Sufuri ta Najeriya (NARTO) reshen Bali, ya ce motar ta yi taho-mu-gama da wata tirela yayin da take ƙoƙarin wuce wata kwana mai hatsari kusa da ƙauyen Kabarin Baturi a hanyar Bali zuwa Serti.
Ya ce dukkanin mutanen da abin ya shafa sun rasu nan take.
Jami’an NARTO, ’yan sanda da wasu jama’a sun taimaka wajen kai gawarwaki da waɗanda suka jikkata zuwa Babban Asibitin Bali.
Lukman, ya bayyana cewa motar an ƙera ta ne domin ɗaukar mutum shida kacal, amma ana cika ta da mutane har tara saboda tsadar mai.
Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Taraba, ASP Victor Mshelizah, ya ce zai yi bayani kan lamarin, amma bai mayar da martani ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.
A Jihar Edo kuwa, mutum 12 ne suka rasu, yayin da wasu 14 suka jikkata a wani hatsari daban da ya auku a ƙarshen mako a ƙauyen Egono da ke hanyar Auchi zuwa Ewu zuwa Benin.
Hatsarin ya auku ne lokacin da wata babbar mota mai ɗauke da fasinjoji da kaya ke gudu, ta yi yunƙurin wuce wata mota ta hannun da bai dace ba.
Motar ta kwacewa direban, lamarin da ya sa ta kife tare da danne mutanen da ke cikinta.
Mai magana da yawun Hukumar Kiyaye Hadura ta Ƙasa (FRSC) a Jihar Edo, Patricia Onwochei, ta tabbatar da faruwar hatsarin, tana mai cewa tukin ganganci ne ya haddasa hatsarin.
Ta ce an riga an binne ɗaya daga cikin waɗanda suka rasu, yayin da aka kai sauran gawarwakin mutum 11 zuwa ɗakin ajiye gawa na Asibitin St. Lazarus.