’Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane a Kaduna
Majiyoyi daga yankin sun ce wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kutsa cikin unguwar ba tare da harbe-harbe ba,
‘Yan bindiga
Al’ummar Karamar Hukumar Kachia da ke jihar Kaduna sun shiga fargaba bayan wani hari da aka kai musu inda aka yi awon gaba da mutum huɗu a Unguwar Mother Cat da ke gundumar Kachia Urban.
Wani Jami’in Tsaron Sa Kai da ya buƙaci a sakaye sunansa ya shaidawa wakilinmu cewa lamarin ya faru ne a ranar Laraba da daddare tsakanin ƙarfe 9:00 zuwa 10:00.
Majiyoyi daga yankin sun ce wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kutsa salin alin cikin unguwar ba tare da harbe-harbe ba, inda suka kwashe kusan awa guda suna gudanar da aikin nasu bayan sun bi ta kusa da makarantar GSS Kachia, inda suka kai hari kan gidaje biyu kacal.
Wani mazaunin garin ya tabbatarwa da wakilinmu cewa mutum huɗu ne aka yi awon gaba da su.
Wakilinmu ya yi ƙoƙarin jin ta bakin rundunar ’yan sandan jihar Kaduna don ƙarin haske bai yi nasara ba, har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.