Gudun hijirata daga Côte D’Ivoire ta kawo karshe —Soro

A baya dai Soro ya kasance na hannun damar Shugaba Alassane Ouattara kafin daga baya su raba gari.

Gudun hijirata daga Côte D’Ivoire ta kawo karshe —Soro

Tsohon Firaministan Cote d’Ivoire, Guillaume Soro, wanda aka yanke wa hukuncin daurin rai-da-rai kan laifin zagon kasa ga tsaron kasar, ya ce ya kawo karshen zaman gudun hijira da ya fara a 2019. 

A baya Soro ya kasance na hannun daman Shugaba Alassane Ouattara, amma a 2019 akalarsu ta yi tsami, inda shugaban kasar ya zarge shi da haifar da tashe-tashen hankula.

Daga nan Soro ya yi gudun hijira, kuma wata kotu ta yanke masa hukuncin daurin rai da rai a 2021.

“Ina sanar da cewa yanzu na kawo karshen gudun hijirata saboda yana da wahala a gare ni na zauna nesa da kakannina da asalina Afirka,” in ji Soro a wani jawabi da aka buga a shafukan sada zumunta.

“Na ki yarda na zama mai laifi. Ban aikata laifin ba, “in ji shi, yayin da ya ce yana so ya bai wa kasar gudunmawa.

Soro ya ce an yi yunkurin kama shi a filin jirgin saman birnin Santanbul na kasar Turkiyya a ranar 3 ga watan Nuwamba, domin mika shi ga Cote d’Ivoire.

Tsohon shugaban ‘yan tawayen da ke iko da rabin arewacin Cote d’Ivoire a farkon shekarun 2000 ya ba wa Ouattara goyon bayan soji yayin fafatawa da tsohon Shugaba Laurent Gbagbo, wanda aka hambarar da gwamnatinsa a 2011 bayan wani mummunan rikici da ya barke bayan zaben.

Daga nan Soro ya zama Firaminista na farko na Ouattara kuma a 2012 aka nada shi kakakin majalisar dokokin kasar.

An kuma yanke wa Soro hukuncin daurin shekara 20 a watan Afrilun 2020 saboda laifin satar dukiyar jama’a.