NAJERIYA A YAU: Amafani Da Karfin Soji Ko Tattaunawa Ne Zai Kawo Matsalar Tsaro A Najeriya?
Muhawara ya kaure kan hanyoyin da suka kamata Gwamnati ta yi amfani da su don kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya. Wasu na ganin amfani da bakin bindiga ita ce hanya daya tilo, wasu kuwa na ganin idan aka tattauna tare da shiga yarjejeniya da ‘yan bindigan ma ba’a ci baya ba, wasu kuwa na ganin idan aka yi amfani da dukkan hanyoyin da zai kawo karshen matsalar shine zai kawo karshen satar mutane don kudin fansa, hare-hare da sauran matsalolin tsaro a Najeriya.
A cikin shekarun nan, matsalolin tsaro a Najeriya—kamar ta’addanci, da garkuwa da mutane, da rikicin manoma da makiyaya, da kuma ayyukan ’yan bindiga—suna kara ta’azzara, lamarin da ya sanya al’umma da masana tsaro ke tambayar wace hanya ta fi dacewa gwamatani ta yi amfani da shi wajen kawo karshen wadannan matsaloli da suka ki ci suka ki cinyewa tsawon shekaru.
Yayin da wasu ke ganin amfani da karfin soji ne kadai hanyar da zai kawo karshen wannan matsala, wasu na ganin tattaunawa ne kadai mafita, wasu har ila yau na ganin idan aka yi amfani da gaurayen biyun zai fi dacewa.
- NAJERIYA A YAU: Irin Radadin Da Masu Cutar Amosanin Jini Ke Fuskanta
- DAGA LARABA: Shin Ya Kamata A Biya Kudin Fansa Ga Masu Garkuwa Da Mutane?
Ko wanne daga cikin wadannan hanyoyi ne idan gwamnati ta yi amfai dashi ko da su don magance wannan matsala?
Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai.
Domin sauke shirin, latsa nan