NAJERIYA A YAU: Dalilan Malaman Jami’oi Masu Zaman Kansu Na Shiga Ƙungiyar ASUU

Wasu na ganin wannan sabon yunƙuri zai iya zama sabuwar hanyar ƙarfafa haɗin kai tsakanin malamai, yayin da wasu ke gargaɗin cewa hakan na iya kawo tsaiko ga karatun ɗalibai da ke ƙaurace ma jami’oin gwamnati sakamakon yawan yajin aiki da suke tsunduma

NAJERIYA A YAU: Dalilan Malaman Jami’oi Masu Zaman Kansu Na Shiga Ƙungiyar ASUU

ASUU

A yayin da tattaunawa kan makomar Ƙungiyarsu Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ke ci gaba da ɗaukar hankali, batun yadda za a shigo da jami’o’i masu zaman kansu cikin ƙungiyar ya kunno kai.

Wasu na ganin wannan sabon yunƙuri zai iya zama sabuwar hanyar ƙarfafa haɗin kai tsakanin malamai, yayin da wasu ke gargaɗin cewa hakan na iya kawo tsaiko ga karatun ɗalibai da ke ƙaurace ma jami’oin gwamnati sakamakon yawan yajin aiki da suke tsunduma lokaci zuwa lokaci.

Wannan shi ne batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai.

Domin sauke shirin, latsa nan