NAJERIYA A YAU: Gaskiyar lamari kan irin noma da aka canza ƙwayoyin halittarsa (GMO)
Shin ko kun san tasirin canza wa irin noma ƙwayoyin halitta da kuma yadda hakan ke shafar lafiyarku?
Alamu na nuna cewa galibin manoma a Najeriya suna da shakku a kan amfani da irin noma da aka sauya ƙwayoyin halittarsa.
Manoma sun shiga tsaka mai wuya sakamakon yadda wasu masana suka yi game da alfanun wannan iri wanda ake kira GMO ko Genetically Modified Organism a turance.
A gefe guda kuma, wasu masana sun yi gargaɗi game da illolin irin.
- NAJERIYA A YAU: Shin Ya Kamata A Samar Da Dokokin Da Za Su Sa Ido Kan Amfani Da AI?
- DAGA LARABA: Yadda sunayen zamani ke neman kawar da na Hausawa
Ko mece ce gaskiya game da amfani da wannan iri na GMO?
Domin sauke shirin, latsa nan