NAJERIYA A YAU: Halayen Da Ambasadoji Ya Kamata Su Mallaka Kafin Tura Su Wasu Kasashe
Irin halayen da ya kamata jakadun dake wakiltar Najeriya a kasashen duniya ya kamata su mallaka tare da nunawa.
A mafi yawan ƙasashen duniya, ana ɗaukar jakadu a matsayin fuskar ƙasa kuma ginshiƙan hulɗar diflomasiyya.
Saboda haka, akwai muhimman halaye da suke tilas jakadan ƙwarai ya mallaka domin ya wakilci ƙasarsa cikin mutunci da nagarta da ƙwarewa.
Tun bayan da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya miƙa sunayen jakadu da yake neman Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta tantance ne dai batun ke ta shan suka daga manazarta kan sunayen da ya gabatar.
Ko waɗanne irin halaye ya kamata jakada ya mallaka a yayin da za a tura shi a matsayin wakili a wata ƙasa?
- NAJERIYA A YAU:Waiwaye Kan Irin Gudunmawar Da Sheikh Dahiru Bauci Ya Bayar Ga Cigaban Addini
- DAGA LARABA: Shin Ya Kamata A Biya Kudin Fansa Ga Masu Garkuwa Da Mutane?
Wannan shi ne batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai.
Domin sauke shirin, latsa nan