NAJERIYA A YAU: Halin da matan da aka yi garkuwa da suke ciki

Shirin Najeriya A Yau ya yi duba ne kan irin rayuwar da matan da aka yi garkuwa da su ke shiga.

NAJERIYA A YAU: Halin da matan da aka yi garkuwa da suke ciki

Sau da yawa matan da aka yi garkuwa da su kan shiga halin ƙunci ko da bayan sun kuɓuta.

Yayin da kaɗan daga cikinsu ke komawa gudanar da rayuwarsu yadda ya kamata, wasu da dama kan tsinci kansu cikin halin damuwa da tagayyara.

Shirin Najeriya A Yau na wannan lokacin ya yi duba ne kan wannan batu da irin shawarwarin da za a ba su don fita daga irin wannan ƙangi.

Domin sauke shirin, latsa nan