NAJERIYA A YAU: Halin Kunci Da Wadanda Hare-haren Ta’addanci Ya Rutsa Da Su Ke Ciki

Halin kunci da damuwa da da wadanda ke fuskantar hare-haren ‘yan ta’adda ke ciki a wasu jihohin Najeriya.

NAJERIYA A YAU: Halin Kunci Da Wadanda Hare-haren Ta’addanci Ya Rutsa Da Su Ke Ciki

A yau, ta’addanci ya zama babban kalubale ga tsaron rayuka da dukiyoyi, ya raba iyalai, ya tilasta dubban mutane barin gidajensu, ya hana yara zuwa makaranta, kuma ya durƙusar da tattalin arzikin yankuna da dama.

Baya ga haka, ta’addanci ya bar raunuka masu zurfi na damuwa da tsoro a zukatan waɗanda suka tsira, wanda sau da yawa ba sa samun kulawar kwararru.

Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan yadda hare-haren ta’addanci ya shafi rayuwar alumma da dama.

Domin sauke shirin, latsa nan