NAJERIYA A YAU: Yadda matsalar tsaro ke mana mu tafiye-tafiyen Kirsimeti
Yayin da bukukuwan karshen shekara ke kara karatowa, ‘yan Najeriya da da suka saba tafiye-tafiye a karshen shekara a wannan lokaci suna bayyana cewa duba da yanayin tsaro sun gwammace su tura da wani abu gida da yin tafiyar.
A ’yan shekarun nan, lokaci na bukukuwan ƙarshen shekara—wanda a da ake ɗauka a matsayin lokacin farin ciki, da haɗuwa da iyalai, da tafiye-tafiye—ya fara sauya salo ga mutane da dama.
Maimakon shirye-shiryen ziyartar ’yan uwa ko halartar bukukuwa a garuruwa daban-daban, mutane da yawa yanzu suna cike da fargaba da damuwa. Babban dalilin hakan shi ne ƙalubalen tsaro da ke ƙara tsananta a sassa daban-daban.
Rahotanni na hare-haren ’yan bindiga, da sace-sace a kan manyan hanyoyi, da garkuwa da mutane, da rikice-rikicen da ke faruwa ba zato ba tsammani, sun sanya mutane da yawa sake tunani kafin su ɗauki hanya da sunan zuwa bukukuwan karshen shekara.
Wannan yanayi ya sa wasu ke zaɓar zama a garuruwan da suke, wasu kuma suna rage nisan tafiya ko sauya tsare-tsaren bukukuwansu gaba ɗaya.
- NAJERIYA A YAU: Alfanu Da Kalubalen Sabon Jadawalin Karatun Makarantu Da Gwamnati Ta Bijiro Dashi
- DAGA LARABA: Ko Ziyarar Tawagar Amurka Za Ta Kawo Karshen Matsalar Tsaro A Najeriya?
Ko yaya bukukuwan wannan shekarar za su kasance?
Wadanne matakai hukumomi ke dauka don kare lafiyan matafiya?
Wadannan da ma wasu tambayoyin shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi kokarin amsawa.
Domin sauke shirin, latsa nan