NAJERIYA A YAU: Matsalar Kansar Mama Da Hanyoyin Magance Ta

So da yawa mata na shiga cikin matsanancin halin cutar kansar mama musamman idan ba a gano cutar da wuri ba, wanda hakan ke jawo yanke maman gaba dayan sa a wasu lokuta.

NAJERIYA A YAU: Matsalar Kansar Mama Da Hanyoyin Magance Ta

Cutar kansar mama na ɗaya daga cikin manyan cututtukan da ke addabar mata a Najeriya da ma duniya baki ɗaya.

 

An kiyasta cewa mata sama da dubu ɗari biyu na kamuwa da cutar a kowace shekara a Najeriya, yayin da miliyoyin mata a duniya ke fama da wannan cuta. Abin damuwa shi ne cewa yawancin lokuta ana gano cutar ne a kurarren lokaci, wanda hakan ke sa magani ya yi wahala kuma ya rage yiwuwar ceto rayuwar wanda ya kamu da shi.

Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai.

Domin sauke shirin, latsa nan