NAJERIYA A YAU: Matsalolin Da Suke Tarnaki Ga Ƙananan Yara A Najeriya Da Hanyoyin Magance Su

Hukumar UNICEF ta ce, kusan rabin yara a Najeriya suna fuskantar ƙalubale, kama daga cin zarafi zuwa rashin samun kulawa da dai sauran su

NAJERIYA A YAU: Matsalolin Da Suke Tarnaki Ga Ƙananan Yara A Najeriya Da Hanyoyin Magance Su

Najeriya tana cikin ƙasashen da suka fi yawan yara a duniya, a cewar Hukumar Kula da Ƙananan Yara ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF).

Sai dai a cewar Hukumar ta UNICEF, kusan rabin waɗannan yara suna fuskantar ƙalubale, kama daga cin zarafi zuwa rashin samun kulawa da dai sauran su.

Wadannan matsaloli da yara suke fuskanta dai sun daɗe suna ci wa masu ruwa da tsaki tuwo a ƙwarya.

Yayin da ake bikin Ranar Yara ta Duniya, shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kan halin da ya yara suke ciki a yau.

Domin sauke shirin, latsa nan