NAJERIYA A YAU: Mummunan Tasirin Rashin Bambance Zazzabin Lassa Kan Lafiyar Al’umma
shin ko kun san illar rashin bambance zazzabin lassa da sauran nau’uka na zazzabi? Ku biyo mu a cikin shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci don warware zare da abawa.
A cewar masana harkar kiwon lafiya, rashin tantancewa balle a bayar da kulawar da ta dace a kan lokaci na cikin dalilan ta’azzarar barazanar da Zazzabin Lassa ke yi ga bangarori da dama na rayuwar al’ummar Najeriya, musamman a yankunan karkara.
Wani bincike a kan tasirin Zazzabin Lassa a kan rayuwar ‘’yan Najeriya wanda aka wallafa bara a mujallar Springer ya nuna gudunmawar da jahilci yake taimakawa wajen yaduwar cutar a kasar.
A sassan Najeriya da dama dai, ba kasafai mutane ke iya bambance Zazzabin Lassa da sauran nau’ukan zazzabi ba.
Shin yaya za a iya gane Zazzabin Lassa a kuma bambance da sauran nau’ukan zazzabi?
- NAJERIYA A YAU: Yadda Ayyuka Suka Ragu A Jihohi Bayan Kudin Shiga Ya Karu
- DAGA LARABA: Me Ke Sa Matasa Zama Karnukan Farautar ‘Yan Siyasa A Kafafen Sadarwa Na Zamani?
Wannan shi ne batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai.
Domin sauke shirin, latsa nan