NAJERIYA A YAU: Shin Da Gaske Irin GMO Na Da Matsala Ga Amfanin Noma A Najeriya?
Takaddama ya kaure kan alfanu ko akasin haka kan amfani da irin GMO a Najeriya. Shin ko Yaya gaskiyar batun yake? Shirin Najeriya A Yau ya yi duba kan wannan batu.
Alamu na nuna cewa galibin manoma a Najeriya suna da shakku a kan amfani da irin da aka sauya ƙwayoyin halittarsa.
Hakan dai na faruwa ne duk da bayanan da wasu masana suka yi game da alfanun wannan iri wanda ake kira GMO ko Genetically Modified Organism a turance.
Tuni dai wasu masanan, waɗanda suka shirya wani taron bita ga manema labarai, suka yi gargaɗi game da illolin irin.
- NAJERIYA A YAU: Dalilan yaduwar cututtuka a lokacin damina
- DAGA LARABA: Asarar Da Hausawa Ke Tafkawa Sakamakon Bacewar Tatsuniya
Ko mece ce gaskiya game da amfani da wannan iri na GMO?
Domin sauke shirin, latsa nan