NAJERIYA A YAU: Tasirin Takardun Shaida Na Bogi Ga Rayuwar Al’umma
Takardun shaida na bogi na daga cikin matsaloli da ke kara addabar Najeriya a fannoni da dama. A wasu lokuta ana samun mutane da ke amfani da takardun karatu ko na ƙwarewa da ba su cancanta da su ba domin samun aiki, muƙami, ko wasu fa’idodi da suka keɓanci waɗanda suka cancanta. Wannan dabi’a ta […]
Takardun shaida na bogi na daga cikin matsaloli da ke kara addabar Najeriya a fannoni da dama.
A wasu lokuta ana samun mutane da ke amfani da takardun karatu ko na ƙwarewa da ba su cancanta da su ba domin samun aiki, muƙami, ko wasu fa’idodi da suka keɓanci waɗanda suka cancanta.
Wannan dabi’a ta zama barazana ga ci gaban ƙasa da amincin al’umma, domin tana lalata tsarin ilimi, rage darajar masu gaskiya, da haifar da rashin inganci a wuraren aiki.
Haka kuma, tana haifar da rashin amincewa tsakanin gwamnati da jama’a, da kuma tsakanin mutane.
- NAJERIYA A YAU: ‘Halin Kunci Ya Sa Muke Zama A Baca A Abuja’
- DAGA LARABA: Tasirin Bambance-bambance Tsakanin ‘Yan Najeriya Shekara 65 Da Samun ‘Yancin Kai
wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai.
Domin sauke shirin, latsa nan