NAJERIYA A YAU: Tinubu ya yi wa Arewa adalci a ayyuka da mukamai — Bayo Onanuga
shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci yayi duba ne kan martanin da mai taimakawa shugaban kasa na musamman kan kafofin yada labarai Bayo Onanuga yayi ga Kungiyar Tuntuba ta Arewa ACF.
Kungiyar Tuntuba ta Arewa (ACF) ta zargi Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu da kin yin adalci wurin ayyuka da raba mukamai tsakanin Arewa da Kudancin Kasar nan.
Wadannan zarge-zarge suka sa fadar Shugaban Kasa ta hannun mai taimaka masa na musamman kan kafofin yada labarai Bayo Onanuga mayar da martani ga kungiyar ta ACF.
Ko wadanne irin martani fadar shugaban kasar ta mayar ga kungiyar?
- NAJERIYA A YAU: Yadda Za A Dama Da Matan Arewa A Fannin Kimiyya
- DAGA LARABA: Dalilan al’ummomi na rungumar gwaji kafin aure
Wannan shi ne batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai.
Domin sauke shirin, latsa nan