NAJERIYA A YAU: Wadanne Kalubale Gwamna Fubara Zai Fuskanta Bayan Dawowa Mulkin Ribas?
Ko wadanne irin kalubale ne ke gaban gwamna Siminilaye Fubara bayan dawowarsa karagar mulkin jihar Ribas?
Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara
A yau ne Gwamna Siminalaye Fubara ke dawowa kujerarsa a matsayin gwamnan Jihar Ribas bayan dakatarwa da ayyana dokar ta baci na watanni shidda da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi a jihar.
Manazarta dai na hasashen wannan dawowar zata bude wani sabon babi a siyasar jihar Ribas.
- NAJERIYA A YAU: Matsayin Doka Kan Hawa Mumbari Ba Tare Da Izinin Gwamnati Ba
- DAGA LARABA: Dalilan Tashin Farashin Doya A Wasu Kasuwannin Najeriya
Yayin da wasu ke ganin gwamna Fubara zai koma bakin aiki ne ya cigaba da gudanar da mulkin jihar kamar yadda ya barta, wasu kuwa gani sukeyi akwai babban kalubale dake gaban gwamnan.
Domin sauke shirin, latsa nan