NAJERIYA A YAU: Yadda Masu Yi Wa Kasa Hidima Za Su Ci Arzikin Yankunan Da Suke AIki
shin ko matasan da ake turawa sassa daban daban na kasar nan hidimtawa kasa na cin gajiyar inda aka tura su? Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya yi duba ne kan yadda masu hidimtawa kasa za su ci gajiyar wuraren da ake turasu a Najeriya.
Bayan hadin kai da karfafa fahimtar juna wadanda hidimar kasa take kawowa, akan samu wasu masu hidimar da sukan yi amfani da duk wata dama da suka samu don neman na sakawa a bakin salati.
Yayin da wasu masu hidimar kasa sukan kama sana’a ko su saka hannun jari a inda aka tura su, wasu kuwa komawa garuruwansu suke yi bayan sun kammala.
- NAJERIYA A YAU: Nasarori da ƙalubalen da Bankin Musulunci ke fuskanta a Najeriya
- DAGA LARABA: Yadda Shara Ke Neman Binne Manyan Biranen Najeriya
Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan irin damar da masu yi wa kasa hidima suke da ita a garuruwan da aka tura su.
Domin sauke shirin, latsa nan