NAJERIYA A YAU:Waiwaye Kan Irin Gudunmawar Da Sheikh Dahiru Bauci Ya Bayar Ga Cigaban Addini
Waiwaye kan gudunmawar da Marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauci Ya bada ga cigaban addini da al’umman Musulmi.
Marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi
Sheikh Dahiru Usman Bauchi, fitaccen malamin addinin Musulunci, masanin tafsiri, kuma jagoran darikar Tijjaniyya, shahararre ne saboda iliminsa mai zurfi da tasirin da ya yi a fagen addini da tarbiyya a Najeriya da ma ƙasashen Yammacin Afirka.
Sheikh Dahiru Bauci ya shafe sama da shekaru saba’in yana koyar da ilimi, ya gudanar da tarukan tafsiri a duk shekara, ya gina makarantu, ya kafa cibiyoyi, kuma ya ba da ilimi ga dubban almajirai hanyoyin da suka taimaka wajen yaɗa ilimin addini cikin lumana da biyayya ga Allah Madaukakin Sarki. Rayuwarsa ta kasance tsantsa ta tsoron Allah, tawali’u, da ayyukan alheri.
- NAJERIYA A YAU: Amafani Da Karfin Soji Ko Tattaunawa Ne Zai Kawo Matsalar Tsaro A Najeriya?
- DAGA LARABA: Shin Ya Kamata A Biya Kudin Fansa Ga Masu Garkuwa Da Mutane?
A wannan waiwayen, za mu duba manyan abubuwa da suka yi fice a cikin rayuwar marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauci da irin tasirin sa ga al’umma, da darussan tafsirin Alƙur’ani da ya yi wa duniya, da irin irin kyawawan dabi’u da ya bari a matsayin abun gado ga musulmi.
Domin sauke shirin, latsa nan