NAPTIP ta ceto mata 5 da aka yi safarar su a Gombe

An yi safararsu ne daga Numan a Jihar Adamawa ba bisa ƙa’ida ba, sannan aka bi ta Legas kafin a kai su Ghana.

NAPTIP ta ceto mata 5 da aka yi safarar su a Gombe

Hukumar da ke yaƙi da fataucin mutane ta Najeriya (NAPTIP), reshen Jihar Gombe, ta ceto wasu mata biyar ’yan asalin Jihar Adamawa da ake shirin kai su ƙasar Ghana domin cin zarafin su ta hanyar karuwanci.

Lamarin na zuwa ne yayin da wani ɗan majalisar dokokin Jihar Adamawa ya yi alƙawarin ƙara ƙaimi wajen yaƙi da fataucin mutane.

Kwamandan NAPTIP na Jihar Gombe, Aminu Muhammad Shira ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Gombe, inda aka miƙa waɗanda aka ceton ga ɗan majalisar da ke wakiltar mazabarsu a Majalisar Dokokin Jihar Adamawa.

Shira ya ce, an cafke matan, masu shekaru tsakanin 20 zuwa 25, a tashar mota ta Ibrahim Hassan Dankwambo Mega Park da ke Gombe, ta hanyar haɗin gwiwar jami’an tsaro daban-daban.

A cewarsa, an yi safararsu ne daga Numan a Jihar Adamawa ba bisa ƙa’ida ba, sannan aka bi ta Legas kafin a kai su Ghana.

Ya ƙara da cewa, binciken farko ya nuna cewa an yi shirin kai su ne domin cin zarafin su ta hanyar karuwanci.

Shira ya bayyana cewa hukumar ta ba su mafaka na wucin gadi, kulawar lafiya, shawarwari da sauran tallafi, yana mai cewa a halin yanzu suna cikin ƙoshin lafiya.

“A matsayinmu na hukuma, muna aiki don haɗa su da iyalansu tare da tallafa musu wajen murmurewa da komawa rayuwa ta gari,” in ji shi.

Ya kuma bayyana cewa, an kama mutum guda da ake zargi da hannu a lamarin, yayin da ake ci gaba da neman sauran ’yan ƙungiyar masu safarar mutane da ake zargin suna aiki tsakanin Najeriya da Ghana.

Kwamandan ya buƙaci jama’a da su kasance masu lura tare da kai rahoton duk wani motsi mai kama da wannan ga jami’an tsaro.

A nasa jawabin, Ɗan majalisar da ke wakiltar mazaɓar Numan a Majalisar Dokokin Jihar Adamawa, Rt. Hon. Pwamwakeno Mikelson Mackondo, ya nuna damuwa kan yawaitar safarar mutane, musamman a tsakanin matasa.

Ya bayyana lamarin a matsayin abin tayar da hankali, tare da kira ga haɗin gwiwar al’umma domin kawo ƙarshensa.